Hoton mikiya ya ci gasa

Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Hoton da ya yi na daya a gasar hotunan da aka dauka da jirage marasa matuka

Bazuwar fasahar kirkirar jiragen sama marasa matuka cikin sauki—da ma na'urorin daukar hoto kanana, marasa nauyi—ta taimaka wajen samar da wani sabon nau'i na daukar hoto da fina-finai.

Kuma wata gasa da mujallar National Geographic ta shirya ta kara fitowa fili da wadansu hotuna masu ban sha'awa da aka dauka da jiragen a shekara guda da ta gabata.

Hoton da ya yi na daya a gasar shi ne hoton wata mikiya da ke shawagi a sararin samaniyar wani gandun daji da ke Indonesia.

Za a iya kallon wadansu hotunan a shafin Dronestagram, wato wani shafin intanet da ya mayar da hankali wajen wallafa hotunan da aka dauka ta sama.

Wanda ya kirkiri shafin, Eric Dupin, ya shaida wa BBC cewa a zahiri hotunan jirage marasa matuka sun samar da wata sabuwar mahanga ta kallon duniya.

"Sun ba da damar kallon duniya ta wata sabuwar mahanga, ta hanyar hotuna na ban-mamaki", inji shi.

Ya kuma kara da cewa hotunan "suna da bambanci matuka da hotunan da tauraron dan-Adam, ko jiragen sama, suka dauka".

Karin bayani