'Hare-haren Isra'ila sun fi shafar fararen hula'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jami'an Palasdinawa sun ce Isra'ila ce ke fara kai hari.

Wata hukuma ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce kashi uku cikin hudu na Falasdinawan da aka kashe a hare-hare ta sama da Isra'ila ke kaiwa Zirin Gaza, fararen hula ne.

Falasdinawa sun ce an kashe mutanen da suka kai dari da ashirin zuwa yanzu.

Ita dai Isra'ila na cewa tana kai hare haren ne a kokarin hana mayakan kungiyar Hamas harba rokoki cikin Isra'ila.

Wani wakilin Hamas Osama Hamdan ya ce ba za samu masalaha ba har sai Israila ta daina kai hare-hare

Karin bayani