Isra'ila ta kai hari tsawon dare a Gaza

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daga cikin wadanda aka kashe a daren jiya har da matasa biyu nakasassu

Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza cikin dare, al'amarin da ya sa adadin Falasdinawan da suka rasa rayukansu ya kai 121.

A rudani da hargitsin da ke tattare da hare-haren cikin dare abu ne mai wahala a iya tantance dukkanin mutanen da aka kashe, da wadanda suka yi rauni, da ma irin barnar da aka yi.

Amma jami'an lafiya na Falasdinu sun ba da rahoton cewa wani gini da aka kaiwa hari a garin Beit Lahiya wata kungiyar bayar da agaji ga nakasassu ce ke amfani da shi.

An kuma ce an kashe biyu daga cikin mutanen da ake kula da su a wurin wadanda matasa ne 'yan shekaru goma sha.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da aikin jin kai ya kiyasta cewa kashi 77 cikin 100 na mutanen da aka kashe a Gaza zuwa yanzu farar hula ne.

Su ma Falasdinawa sun ci gaba da harba rokoki daga Gaza, kuma da tsakar dare an ji jiniyar da ke gargadin cewa an harbo makami a yankuna akalla biyu na kudancin Isra'ila.

An dai ce yanzu haka jami'an diflomasiyya na wata tattaunawa a Majalisar Dinkin Duniya, sai dai har yanzu babu alamun cewa sun dau hanyar gano bakin zaren tsagaita wuta wanda bangarorin biyu za su amince da shi.

Karin bayani