Isra'ila ta kai hari kan shugaban tsaro

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Galibin wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren na Isra'ila farar hula ne

Jami'an Falasdinu sun ce an kashe mutane akalla 15 lokacin da Isra'ila ta kai wadansu sababbin hare-hare a kan gidan shugaban 'yan sanda na zirin Gaza.

An bayar da rahoton cewa shugaban 'yan sandan, Tayseer Al-Batsh, ya jikkata a harin.

An kai hare-haren ne bayan da kungiyar Hamas ta yi barin rokoki masu cin dogon zango a kan biranen Isra'ila, ciki har da Tel Aviv.

Jami'an Isra'ilar sun ce an kuma harba rokoki biyu arewacin kasar daga Lebanon, amma sun fada wadansu yankuna inda babu kowa.

Don mayar da martani Isra'ila ta kai hari a cikin kasar ta Lebanon, al'amarin da ya jawo fargabar cewa rikicin ka iya fadada.

A cikin dare kuma, sojojin kasa na Isra'ila, wadanda dakarun kundunbala ne na rundunar sojin ruwan kasar, sun shiga zirin Gaza a karo na farko.

Sun kuma kai samame ne a kan wani wuri da ake zaton maboya ce ta makaman roka masu cin dogon zango na Hamas.

Isra'ila ta ce hudu daga cikin sojojin sun yi rauni a musayar wutar da suka yi da mayakan Hamas; amma kungiyar ta Hamas ta ce sojojin na Isra'ila ba su kai labari ba.

Kusan Falasdinawa 150 ne suka rayukansu a tashe-tashen hankulan; amma babu wani dan Isra'ila da ya rasa ransa.

Karin bayani