Nigeria: "An gano makamai a Dajin Balmo"

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hedkwatar tsaro ta Nigeria ta ce a wadansu ramuka a cikin Dajin Balmo aka binne makaman

Hedkwatar tsaro ta Nigeria ta ce ta gano karin makamai a cikin Dajin Balmo, wanda ya tashi daga Jihar Bauchi ya dangana da Jihar Jigawa. An kuma ce ya makwabci Dajin Sambisa wanda ke Jihar Borno inda 'yan kungiyar Boko Haram ke da sansanoni.

Wata sanarwa da kakakin hedkwatar tsaron, Manjo Janar Chris Olukolade, ya aikewa BBC ta ce sojoji suna tonon wadansu wurare ne a dajin da nufin gano makaman da aka binne lokacin da suka yi kicibis da manyan bindigogi goma, da bindigogi masu sarrafa kansu fiye da 80, da kuma jigidar harsasai da dama.

Sanarwa ta kara da cewa an kuma gano makaman harba rokoki da sauran kayan yaki masu yawa.

Janar Olukolade ya kuma ce sojoji sun gano kayan jami'an tsaro ciki har da rigar kariya daga harbin bindiga.

A ranar Litinin ne dai hedkwatar tsaron ta Nigeria ta bayar da sanarwar cewa dakarunta sun fatattaki wadansu 'yan kungiyar Boko Haram daga Dajin na Balmo.

Hedkwatar tsaron ta kuma ce mutanen da aka kama a cikin dajin yayin fafatawar suna bayar da bayanan da ke alakanta kulle-kullen da ake yi a dajin da wadansu ayyukan ta'addanci a sauran sassan kasar.

Karin bayani