Malaman Poly a Nijeriya sun janye yajin aiki

Kwalejin polytechnic dake Mubi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwalejin polytechnic dake Mubi

Kungiyar malamai ta makarantun kimiyya da fasaha na Najeriya, sun bayyana janye yajin aikin da suka kwashe kimanin shekara daya suna yi.

Bayan wani taro da sabon ministan ilimin kasar ne, Malam Ibrahim Shekarau, kungiyar ta ce daga ranar Talata mai zuwa zata janye yajin aikin, inda ta bada sarari na watanni ukku domin ganin abin da gwamnatin kasar za ta yi dangane da korafe-korafen da ta mika.

Daga ciki akwai batun samar da kayayyakin ayyukan yi, da mayar da darajar takardar shaida ta babbar diploma, HND, ta koma iri daya da digiri na jami'a.