Jamus na da kwarin gwiwar nasara

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Joachim Low na ganin Jamus za ta ba da mamaki

Kociyan Jamus Joachim Low, ya ce yana da kwarin gwiwa cewa 'yan wasansa za su zama tawaga ta farko a Turai da za su sami nasarar cin kofin kwallon kafa na Duniya a Amurka ta kudu.

Jamus za ta kara da Argentina a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a filin wasa na Maracana ranar Lahadi, bayan da ta sami nasara kan Brazil inda ta lallasata da ci 7-1.

Low, ya nanata cewa Jamus ba ta da wani tsoro kan gogaggen dan wasan nan na Argentina Lionel Messi.

Jamus dai rabon ta da ta ci gasar kofin kwallon kafa na duniya tun 1990 lokacin da ta doke Argentina a Rome.

Karin bayani