Malala Yousafzai na ziyara a Nigeria

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Yayin ziyararta a Nigeria, Malala za ta gana da Shugaba Goodluck Jonathan

Ranar Asabar da dare yarinyar nan 'yar Pakistan, Malala, da mahaifinta, Ziauddin Yousafzai, suka sauka a Abuja, babban birnin Nigeria, inda za ta yi bikin cikarta shekara 17 da haihuwa.

Yayin ziyararta a kasar, Malala za ta gana da Shugaba Goodluck Jonthan na Nigeria, da masu fafutukar ganin an kwato 'yan matan Chibok, wato #BringBackOurGirls, da kuma kungiyoyin farar hula masu yekuwar bayar da ilimi ga yara mata.

Dadin dadawa, ana sa ran Malala za ta gana da wadansu daga cikin ''yan matan Chibok da suka kubuto daga hannun wadanda suka sace su, da ma iyayen wadanda suke hannun 'yan Boko Haram har yanzu.

A wata sanarwa da ta fitar, Malala ta ce, "Na zo Nigeria ne don girmama wadannan jaruman 'yan matan da suka sadaukar da rayukansu don su samu ilimi".

Ranar 12 ga watan Yuli ce dai Malala ke cika shekaru 17 da haihuwa, kuma an ayyana ranar a matsayin Ranar Malala ta Duniya.

Shekaru biyu da suka wuce wani dan bindiga da kungiyar Taliban ya harbe ta a ka saboda jajircewarta wajen ganin yara mata sun samu ilimi.

Karin bayani