Southampton ta sayi Graziano Pelle

Image caption Graziano Pelle ya koma Southampton

Kungiyar kwallon kafa ta Southampton ta rattaba hannu a kwantaragi kan dan wasan nan Graziano Pelle daga Feyenoord akan kudaden da ba a bayyana ba.

Dan wasan dan kasar Italiya mai shekaru 29 ya amince da kwantaragin shekaru uku.

Graziano zai sake haduwa da Kociya Ronald Koeman.

Graziano Pelle ya zura kwallaye 55 a wasanni 66 a kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord.

Karin bayani