'Scotland za ta dace da tashar sama jannati'

Image caption Gwamnatin Scotland ta ce 'yancin kai ne kawai zai bunkasa fanninta na harkokin samaniya

Birtaniya ta ce mai yuwuwa a kafa tashar jiragaen zuwa sararin samaniya na 'yan sama jannati.

Hukumomin na Birtaniya suna son samar da tashar nan da zuwa shekara ta 2018.

Idan aka samar da tashar a Scotland hakan zai kasance na farko da za a yi a wajen Amurka.

An ware wurare takwas da za a iyasamar da ita, kuma Scotland na da shida daga ciki.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A farkon makon da ya gabata aka yi nasarar jarraba harba wani tauraron dan adam da wani kamfani da ke Glasgow Clyde Space, ya kera, zuwa sararin samaniya.

Alkaluman da gwamnati ta fitar sun nuna cewa fannin jiragen sama yana daya daga cikin fannonin da suka fi bunkasa a Birtaniya gaba daya.

Labarin zabar Scotland, ya samu karbuwa daga gwamnatin yankin, wadda ta ce hakan zai kara bunkasa fannin.

Sakataren baitulmalin Birtaniya, Danny Alexander, ya ce yankin Scotland zai iya kasancewa cikin tsarin Birtaniya na jiragen safarar jama'a na kasuwa zuwa sararin samaniya.