An kasa samun email a Birtaniya

Image caption Hasumiyar kamfanin sadarwa na Birtaniya

Dubban masu mu'amulla da kamfanin sadarwa na Britaniya BT, sun kasa samun wasikunsu ta intanet na email saboda wani gyara.

Masu amfani da kamfanin sun yi korafin kasa aikewa ko samun wasiku ta intanet daga ranar Juma'a 11 ga watan nan na Yuli har zuwa ranar Litinin da rana.

Matsalar ta taso ne sakamakon aikin da kamfanin yake yi na sauya wa masu amfani da hanyarsa ta sadarwa email dinsu daga kamfanin Yahoo zuwa tasa.

Wasu masu amfani da sadarwar kamfanin sun ce bai sanar da su game da aikin ba kamar yadda ya kamata.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kamafanin na BT, da kansa ya tabbatar cewa wasu wasikun na email sun bace sakamakon matsalar.

Wannan shi ne karo na biyu cikin 'yan makwanni da kamfanin na BT, ke neman gafarar masu mu'amulla da shi.

A karshen watan da ya gabata kamfanin ya nemi gafarar mutane, bayan da masu amfani da intanet dinsa a Birtaniya suka kasa samun intanet.

A watan Maris kwamishinan sadarwa, ya binciki kamfanin sakamakon korafin da ake yi cewa, ya sa bayanan tarin masu amfani da intanet din sa cikin hadarin bayyana ga jama'a.

Wani mai kwarmata bayanai ne ya bayyana damuwar, yayin da kamfanin ke aikin sauya adireshin wasikun intanet na masu amfani da sadarwarsa.