An amince wa mata zama limamai a Coci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zuwa karshen shekara mata za su soma rike mukamin

Majalisar gudanarwar cocin Ingila, Synod ta kada kuri'ar amincewa da nada mata a mukamin manyan limaman coci watau bishop bishop.

Kuri'ar wadda aka kada a York ta share fagen nada mace bishop ta farko a cocin Ingila nan da karshen wannan shekarar.

An kada kuri'ar ne bayan mahawarar sa'o'i biyar da aka tafka a Jami'ar York.

Wannan matakin na zuwa ne shekaru 20 bayan da aka bai wa mata damar samun zama masu wa'azi a coci.

Bukatar nada mata limaman ta samu goyon bayan Archbishop na Canterbury Justin Welby da kuma Firaministan Birtaniya, David Cameron.