Ana yunkurin diplomasiya kan rikicin Isra'ila da Palasdinu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane 172 sun rasu sakamakon luguden da Isra'ila ke kaiwa

Jami'an diplomasiyya daga kungiyar Tarayyar Turai sun bukaci kasashen Isra'ila da Palasdinu da su kai zuciya nesa, su dakatar da bude-wuta a Gaza.

Mahukunta a Amurka dai ba su tabbatar da rahotannin da ke fitowa daga kasar Masar ba, mai cewa Sakataren harkokin wajen Amurkar, John Kerry zai kai ziyara Masar don tattaunawa a kan hanyoyin kawo karshen fadan.

Isra'ila dai na ci gaba da lugude boma-bomai a kan Gaza.

Yayin da kungiyar Hamas kuma ke ruwan rokoki a kan iyakokin Isra'ila.

Palasdinawa dai sun ce sama da mutum dari da saba'in ne aka halaka a fadan, kuma galibinsu farar-hula.

Shugaban kasar Faransa Fransuwa Olan ya ce dole ne dukkan bangarorin su yi hakuri.

Ya ce, "kasar Isra'ila na da 'yancin kare kanta, kuma za ta iya kare kanta idan aka far mata, amma wajibi ne ta kasance mai hakuri wajen daukan mataki."