'2015: Za mu yi zabe a ko ina a Nigeria'

Image caption Farfesa Jega na fuskantar matsin lamba kan 2015

Shugaban hukumar zaben Nigeria INEC, Farfesa Attahiru Jega ya ce Hukumar za ta gudanar da zabuka a ko ina a fadin kasar a zaben 2015.

Shugaban ya ce bai taba cewa ba za a yi zabe a inda ake samun tashe tashen hankula ba.

A baya dai an ta maganar cewa hukumar ba za ta gudanar da zabe a jihohin da ake samun tashe-tashen hankula ba.

INEC na fuskantar matsin lamba a Nigeria game da batun gudanar da sahihin zabe a kasar.

Zabukan shekarun baya a Nigeria na cike da cece-kuce game da zarge-zargen aringizon kuri'u da kuma satar akwatunan zabe.