Chibok: Malala ta ziyarci Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Malala Yousafzai ta ce 'yan matan Chibok 'yan uwanta ne

Yarinyar nan 'yar Pakistan mai fafatukar ci gaban Ilmin 'ya'ya mata Malala Yousafzai, ta gana da shugaban Nigeria Goodluck Jonathan domin matsin lamba a dauki karin matakai don ceto yan matan nan yan makaranta su fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka sace.

Shugaban Boko Haram din ya nanata a wani sabon video cewa a shirye yake na tattauna musayar yan matan da yan uwansu da ake tsare da su a gidajen yari.

A wata ganawa mai muhimmanci da ta gudana a zauren taro na wani babban Otel a birnin Abuja, wasu mashahuran mutane sun hadu wadanda suka hada da mutane 12 iyayen wasu daga cikin 'yan matan nan yan makarantar Chibok wadanda 'yan Boko Haram suka sace watanni ukku da suka wuce.

Wasu muhimman mutane biyu da su ma suka halarci taron su ne Malala Yousafzai yarinyar nan yar Pakistan wadda a yanzu ta cika shekaru 17 a duniya da kuma mahaifinta Ziauddin.

Malala wadda ke cike da damuwa da karfin zuciya ta ce ta zo Nigeria ne daga Birmingham a Ingila inda a yanzu ta ke da zama saboda ta dauki 'yan matan da aka sace a matsayin 'yan uwanta. Ta na mai cewa " Zan tsaya tsayin daka, Ina tare da su."

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Malala tare da mahaifiyar daya daga cikin 'yan matan da aka sace

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar Litinin 14 ga watan Yuli a matsayin ranar Malala, wadda ta cika shekaru 17 da haihuwa, kuma ta yanke kudirin amfani da bikin ranar zagayowar haihuwarta ce wajen zuwa Nigeria domin gabatar da koken ganin an sako yan matan 'yan makaranta da kuma tabbatar da yancin samun Ilmi ga dukkanin yara.

Saboda mu talakawa ne

Ko da yake a baya bayan nan ne Nigeria ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, ita ce kuma mafi koma bayan tarihi a fannin Ilmi inda yara wadanda shekarunsu ya kama daga 6 zuwa 9 kwatankwacin kashi 42 cikin dari basa zuwa makaranta.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwanaki 90 da sace 'yan matan

Hakan nan kuma akwai gibin malaman Firamare fiye da 200,000

Malala ta yi imani akwai dangantaka tsakanin karancin ilmi da kuma tashe tashen hankula masu nasaba da siyasa wadda kungiyar Boko Haram ta kawo Nigeria.

Malala ta yi roko a baiwa dukkanin yara a Nigeria damar samun Ilmi.

Ziauddin Yousafzai ya baiyanawa iyayen yan matan Chibok yadda yan Taliban suka harbi Malala a ka shekaru biyu da suka wuce da kusan hallaka ta. Bai kammala bada labarin ba sai fashe da kuka.

Iyayen 'yan matan Chibok su goma sha biyu wadanda ke sauraronsa su ma sai suka barke da kuka.

Iyayen sun tausaya duk da halin da ciki na rashin ganin yayansu, an bar su ba a kula da su ba. Gwamnati ba ta yi magana da su ba ta kowane hali. Ba ta ma nuna musu wata alamar tausayi ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An yi taro a London da Paris domin kokarin ceto 'yan matan Chibok

Rebecca Samwell ta ce sun ji rade radi cewa wai an ceto wasu daga cikin yan matan da aka sace. Yarta Sarah shekarunta 17 kamar Malala. Tace " A zahirin gaskiya ba a sanar da mu gaskiyar al'amura."

Mallam Abu daya daga cikin iyaye maza yace shin saboda mu matalauciyar kasa ce shi yasa gwamnati ba ta yi komai? Idan da wadannan yara yayan wani babba ne fa? Shin za su ci gaba da kasancewa a cikin daji har bayan kwanaki 90?