Ba mu ga bidiyon Shekau ba —Omeri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban kungiyar Boko Haram ya kuma bayyana goyon baya ga ISIS a bidiyon

Hukumomi a Nigeria sun ce har yanzu ba su ga hoton bidiyo na baya-bayan nan da shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fitar ba.

Ranar Lahadi ne dai shugaban na Boko Haram ya saki bidiyon, wanda a ciki ya ce kungiyar ce ta kai hare-hare a wasu sassan Nigeria da suka hada Kano, da Jos, da Abuja, da kuma Lagos.

A harin na Lagos dai wani abu ne ya fashe a tashar ajiye man fetur da dangoginsa da ke Apapa, hukumomi kuma suka ce hadari ne ya auku.

A wata hira da ya yi da BBC, shugaban cibiyar samar da bayanai ta kasa, Mike Omeri, ya ce babu wata rufa-rufa da hukumomin suka yi dangane da labarin harin na 25 ga watan Yuni a Lagos.

"Ba a boye na ko'ina ba sai na Lagos ne za a boye? Muna ma riga wasu fada idan aka kai hari—wanda muka sani—[saboda haka] ba abin da za a boye", inji Mista Omeri.

Karin bayani