An harbo jirgin Ukraine daga Rasha

Jirgin saman sojin Ukraine da aka harbo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin saman sojin Ukraine da aka harbo

Ukraine ta ce mai yiwa makamin roka da aka harba daga yankin Rasha shine ya kakkabo jirginta na soji a gabashin kasar.

Ministan tsaron Ukraine din ya ce jirgin yana tafiya a tazara mai nisa a sararin samaniya yadda makaman da yan aware magoya bayan Rasha suke amfani da su ba za su iya kaiwa gare shi ba.

Fadar gwamnatin a Kiev ta ce ta lura da taruwar motocin soji a bangaren iyakar Rasha .

Kungiyar tsaro ta NATO ta yi kiyasin cewa Moscow ta jibge sojoji tsakanin dubu goma zuwa dubu goma sha biyu a yankin.

Rasha dai ta musanta tallafawa yan awaren ta kuma gayyaci kungiyar kawancen tsaro da raya tattalin arziki ta nahiyar turai OSCE ta kai ziyara yankunanta biyu da suka iyaka da kasar ta Ukraine.

Karin bayani