An kama dodonkodin Nigeria a Amurka

Hakkin mallakar hoto AP

Jami'an kwastam a Amurka sun kama wasu manya-manyan dodonkodi da aka yi safararsu daga Nigeria.

An kama dodonkodin guda 67 wadda kowannensu ya kai nauyin kusan kilo guda, a filin jiragen sama na Los Angeles.

Mai magana da yawun hukumar kwastam Lee Harty ta ce mutum guda aka yi niyyar kai wa dodonkodin a California.

Dodonkodin na daga cikin wadanda suka fi kowanne girma a duniya, inda su kan girma har tsawonsu ya kai inci takwas, a cewar jami'an.

Ko da yake ana cin dodonkodi a Najeriya, amma Amurka ta hana shigar da su kasarta saboda suna dauke da kwayoyin cuta, ciki har da mai janyo cutar sankarau.

Hakkin mallakar hoto AP

A cewar wata jami'ar shiri kan aikin noma a Amurkar, Maveeda Mirza dodonkodi kan yi barna sosai ga amfanin gona, inda su kan ci duk wani amfanin gonar da suka samu.

Ta kara da cewa ana cigaba da binciken dadlilan da yasa mutum daya ke son duba dodonkodin, amma kuma babu alamun cewa an yi fasakwaurinsu ne zuwa kasar.

Maveeda ta bayyana cewa wannan ne karon farko da aka taba kama dodonkodi mai yawa irin haka, ko da ya ke ana samun kananan da suka fi haka yawa a jakukkunan mutane da suke cewa sun shiga ba da saninsu ba ne.

Hukumomin Amurkan dai sun kone dodonkodin saboda fargabar kada su yada kwayoyin cuta.