Boko Haram: An kashe mutane 45 a Dille

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar na barnata rayuka a Nigeria

Mutane akalla 45 ne suka rasu a kauyen Dille da ke jihar Borno a arewacin Nigeria sakamakon harin da 'yan Boko Haram suka kai a kauyen.

Wasu mazauna kauyen sun ce 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne, suka kai harin a ranar Litinin da safe.

Daya daga cikin mutanen da suka tsira daga harin sun ce an kashe mutane 45 sakamakon harin.

A cewarsa, an kashe fararen hula 25 a yayinda mutane 20 daga bangaren Boko Haram suka gamu da ajalinsu lokacin harin.

Wasu daga mazauna kauyen sun zargin cewar an yi barin wuta da jiragen saman yaki na dakarun Nigeria lokacin da lamarin ya auku, abinda ya janyo rasuwar wasu fararen hula da aka zaci 'yan Boko Haram ne.

Rikicin Boko Haram ya hallaka mutane fiye da 2000 a wannan shekarar.