Ko abokai na da kwayoyin halitta daya ?

Bincike game da kwayoyin halittar dan adam Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bincike game da kwayoyin halittar dan adam

Wani nazari da aka samu daga wasu tagwayen bincike masu cike da rudami a Amurka sun yi ikirarin cewa, mutane suna da kwayoyin halitta iri daya da abokansu fiye da yadda zai kasance da wasu baki.

Bisa la'akari da bambance-bambancen dake tsakanin mutane kimanin dubu biyu da aka zaba a wani bangare na binciken da aka gudanar a wani karamin Kauye na Amurka, masana kimiyyar, sun gano cewar, abokai suna da kwayoyin halitta iri daya da kimanin dakika da digo daya a matsakaici fiye da baki.

Sauran masana kimiyya suna tababa a kan kasidar wadda aka buga a PNAS.

"Ina ganin wasu abubuwa ne da ba kasafai a kan gano ba, kuma yawanci ta kan janyo suka daga masana kimiyya" a cewar Farfesa James Fowler, daya daga cikin mutanen da suka kirkiro binciken kuma Farfesa na fannin kimiyyar kwayoyin halitta da kimiyyar siyasa a Jami'ar California, San diego.

Da shi da Farfesa Nicholas Christakis na Jami'ar Yale, Farfesa Fowler ya yi nazarin mutane kimanin dubu dari biyar masu bambancin kwayar halitta, ta hanyar amfani da bayanai da aka samu daga binciken da aka gudanar a kan zuciya a Framingham.

Wannan sakamakon binciken yana da amfani saboda duk da ya bayar da samfur na kwayoyin halitta, an tambayi wadanda aka zaba domin gwajin ko su wane ne, abokansu na kut-da-kut. Farfesa Fowler ya bayyana cewa "saboda an fara nazarin ne a wata 'yan karamar al'umma, mutanen da aka kira abokai, su ma sun shiga cikin binciken."

Don haka shi, da Farfesa Chiristakis suka kididdige dangantakar ta hanyar amfani da kwayoyin halittar daga wasu abokai da baki, kuma suka gano cewar dan bambancin kadan ne a tsakanin abokai.

"Ba wai lallai muna ikirari ba ne dangane da kwayoyin halittar takamaimai wanda ake binciken a kan sa a nan,"Farfesa Fowler ya gaya ma sashen labarai na BBC. "muna ikirari ne a kan yanayin halayya a dukkan masu kwayoyin halittar iri daya".

Sai dai kuma wadanda suka kirkiro binciken sun yi kokarin bayar da dama ga duk wasu masu dangantaka ta jini a cikin mutanen da suke gudanar da binciken a kan su, a wani binciken makamancin wannan na abokan juna dari da tara a wannan karon wanda ya hada da kimanin mutane miliyan daya da rabi masu kwayoyin halittar dabam-dabam.

Karin bayani