Isra'ila ta gargadi mazauna Gaza su bar gidajensu

Hakkin mallakar hoto na
Image caption Hare haren Isra'ila sun kashe mutane 194 ya zuwa yanzu

Isra'ila ta baiwa dubbban Palasdinawa dake gabashi da kuma arewacin Gaza umarnin su bar gidajensu yayinda take cigaba da kaddamar da hare harenta ta sama.

Gargadin ya biyo bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da Masar ta kirkiro wanda kuma ya kasa dakatar da hare- haren roka akan Isra'ila.

Tun farko Hamas ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita wutar, amma wani jami'i daga bisani ya fadawa BBC cewa zata duba hanyar kawo karshen rikicin a siyasance.

Jami'an Palasdinawa sun ce hare- haren Isra'ila sun kashe mutane 194 ya zuwa yanzu.

A ranar Talata Isra'ila ta bada rahotan wadanda harin Palasdinawan ya shafa mutanenta a karon farko.

Cigaba da kai hare hare ta sama na zuwa ne bayan da Firai Ministan Isra'ilar Benjamin Netanyahu yace ba suda zabi illa iyaka su kara zafafa hare harensu.