Greg Clark na da jan aiki a gabansa

Greg Clark Hakkin mallakar hoto
Image caption Greg Clark masanin tattalin arziki ne

Masu sharhi sun bayyana cewa Greg Clark na da jan aiki a gabansa a matsayin sabon ministan kimiyya na Birtaniya

Mr Clark ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ya yi matukar farincikin nadin da akai masa, kuma zai dora akan aikin da David Willetts ya soma

Zai hada aikin tare da aikinsa na ministan birane.

Daya daga cikin mahimman ayyukansa shine ya ganar da masu bincike cewa ba a ragewa kimiyya mahimmanci ba sakamakon hadewar ma'aikatun biyu.

An cire Owen Paterson daga mukaminsa na sakataren muhalli a garanbawul dinda aka yi.

Liz Truss mai shekaru 38 ne zai karbi aikin daga wajensa

Mr Clark masanin tattalin arziki ne kuma tsohon ministan baitulmali.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption David Willetts ne ya sauka daga mukamin

Fatan da ake yi shine dangantakar Mr Clark tare da Chancellor Goerge Osborne zata zama alheri ga bangaren kimiyya.

Sai dai kuma zai amsa tambayoyi game da shawararsa na goyawa wani kudurin majalisar dokoki baya na samar da wasu magunguna a tsarin lafiya na NHS a shekarar 2007.

Babbar rawar da zai taka ita ce ta sa ido akan yadda ake kashe kudaden da aka ware domin bincike da kuma gudanar da jami'oi.

Yana da wuya dai ya iya koyi da wanda ya gada Mr Willetts- wanda masana kimiyya suka jinjina masa bayan barinsa aiki