Isra'ila ta karbi shirin tsagaita wuta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Isra'ila ta ce ta kai hari a kan wurare kusan 1,000 a zirin Gaza

Majalisar tsaron Isra'ila ta amince da wani shiri na tsagaita wuta a zirin Gaza wanda Masar ta gabatar, bayan da ta tattauna a kansa da safiyar ranar Talata.

Amma wata sanarwa daga bangaraen mayakan Hamsa ta ce shirin ba komai ba ne illa ba da kai bori ya hau. A yanzu dai wadansu majiyoyin Hamas sun ce za a ci gaba da ba-ta-kashi matukar Isra'ila ba ta sako fursunoni, ta hada kai da Masar wajen dage takunkumin da kakakbawa Gaza ta fuskar tattalin arziki ba.

Ma'aikatar harkokin wajen Masar ce dai ta gabatar da shirin ana gab da fara wani taron gaggawa na Kungiyar Kasashen Larabawa a birnin Alkahira.

Shirin tsagaita wutar ya bukaci Isra'ila da Hamas su dakatar da kai hare-hare daga safiyar ranar Talata.

Ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shukry, ya ce wannan shiri na Masar ya ta'allaka ne a kan dakatar da kai hare-hare nan take, da sake bude hanyoyin shiga Gaza, da kuma aiwatar da shirin tsagaita wutar bayan bangarorin sun amince su daina yi wa juna kallon hadirin kaji.

Wannan sanarwa ta Hamas dai ba abu ne mai karfafa zuciya ba, amma kuma ba ya nufin ba za a cimma yarjejeniya ba, sannu dai ba ta hana zuwa.

Karin bayani