Jonathan zai gana da iyayen 'yan Chibok

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Malala ta kuma nemi gwamnatin Najeriya ta ceto 'yan matan ba tare da wani abu ya same su ba

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan zai gana da iyayen 'yan matan Chibok da kuma wasu daga cikin 'yan matan da suka tsere.

Za a yi ganawar ce da iyaye 12 da kuma 'yan matan biyar a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja.

Wannan ce ganawa ta farko tsakanin bangarorin biyu, wadda za a yi watanni uku bayan da kungiyar Boko Haram ta sace 'yan mata 'yan makaranta fiye da 200 a garin Chibok da ke jihar Borno.

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan yarinyar nan 'yar Pakistan da Taliban suka harba, Malala Yousafzai, ta kai ziyara Najeriya, inda ta nemi shugaban ya gana da iyayen 'yan matan na Chibok.