An kai hari a filin jirgin saman Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An lalata jiragen sama da dama

An kai hari da makamin roka a babban filin saukar jiragen sama na Libya, a yayinda fada ya tilasta rufe filin jirgin saman na Tripoli.

Mutum daya ya rasu sannan an lalata jiragen sama 12 a filin saukar jiragen saman na Tripoli.

Kakakin gwamnati ya ce Libya na tunanin neman agaji daga dakarun kasashen wajen domin sake tabbatar da tsaro a kasar.

Shugabannin Libya sun kasa tabbatar da tsaro a kasar tun bayan da aka hambarar da Shugaba Muammar Gaddafi a shekara ta 2011.

A yanzu kasar ta fada cikin rikici tsakanin mayakan sa kai a yayinda gwamna ta kasa shawo kan matsalar.