Malala ta bada gudunmuwar $200,000 a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Malala ta gana da Shugaba Jonathan a Abuja

'Yar Pakistan mai rajin kare hakkin mata ta fuskar ilimi, Malala Yousafzai ta sanarda bada gudunmuwar dala 200,000 na Amurka domin tallafawa ilimin 'ya'ya mata a Nigeria.

Malala ta sanar da bayar da gudunmawar ce a wajen wata lacca da ta gabatar a birnin Abuja albakacin bukin ranar Malala.

Tun a karshen mako Malala ta shiga Nigeria domin tattaunawa da gwamnati kan yadda za a ceto 'yan matan da aka sace a Chibok fiye da watanni uku da suka wuce.

'Yar Pakistan din ta gana da Shugaba Goodluck Jonathan da iyayen 'yan matan da kuma kungiyar #Bringbackourgirls wacce ke fafutukar ganin an kubutar da 'yan matan.

Malala Yousafzai da kyar ta tsira da ranta a hannun 'yan Taliban bayan da suka harbe ta a kai saboda fafutukar da take yi don ganin mata sun sami ilimi a Pakistan.