An kama dodonkodin Nigeria a Amurka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani jami'in kwastam ya ce an kona dodonkodin ba tare da sa tafarnuwa ko mai ba

Jami'an kwastam a Amurka sun kama wasu manya-manyan dodonkodi da aka yi safararsu daga Nigeria.

An kama dodonkodin guda 67 wadda kowannensu ya kai nauyin kusan kilo guda, a filin jiragen sama na Los Angeles.

Ko da yake ana cin dodonkodi a Najeriya, amma Amurka ta hana shigar da su kasarta saboda suna dauke da kwayoyin cuta, har da mai janyo cutar sankarau.

Haka kuma Amurkar ta ce dodonkodi kan yi barna ga amfanin gona kuma yana cin fentin gini.