An kashe mutane 50 a Zamfara

Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Idi Yari Hakkin mallakar hoto zamfara website
Image caption Ana zargin wasu Fulani da kai harin.

Wasu da ake zargin Fulani ne sun kashe fiye da mutane 50 tare da jikkata wasu da dama a gundumar Gidandawa da ke karamar Hukumar Maradun a jihar Zamfara.

Hakan na zuwa ne kwana guda da kashe akalla mutane 10 da ake kyautata zaton suma wasu fulani ne suka hallaka su, a gundunmar Pilgani da ke karamar hukumar Langtang ta arewa a jihar Plateau.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi wa kauyen kawanya ne da misalin karfe 5 na asuba, ka na suka bude wuta ga duk wanda suka gani a lokacin.

Kawo yanzu dai babu wanda ya san dalilin harin, sai dai wata majiyar jami'an tsaro ta bayyana cewa ta yiwu harin na ramuwar gayya ne, saboda maharan Fulanin na takun saka da 'yan kauyen.