Al-Makura: An yi zanga-zanga a Maraba

Hakkin mallakar hoto website nassarawa
Image caption Kujerar Umaru Almakura na rawa

Wasu mazauna unguwar Maraba da ke jihar Nasarawa mai makwabtaka da Abuja sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna adawa da yinkurin tsige Gwamna Umaru Tanko Al-Makura.

Masu zanga-zangar sun nuna goyon bayan Gwamna Al-Makura tare da kira ga 'yan majalisar dokokin jihar su kawar da yinkurin tsige gwamnan daga mukaminsa.

A ranar Litinin ne Majalisar Dokokin jihar Nasarawa ta baiwa akawun majalisar umurnin ya mika wa Gwamna Al-Makura takardar bukatar tsige shi bisa zargin almubazzaranci da dukiyar al'umma da kuma saba ka'idar aiki.

'Yan majalisa 20 na jami'yyar PDP ne suka sanya hannu a bukatar tsige gwamnan a yayinda sauran 'yan majalisa hudu na jam'iyyar APC suka ki sanya hannu.

Hakan na zuwa a daidai lokacin da 'yan majalisar dokoki suka tsige gwamna Murtala Nyako na jihar Adamawa.

Karin bayani