Boko Haram: Nigeria ta kafa asusun tallafi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan Najeriya ne ke gudun hijira a ciki da wajen kasar saboda rikicin Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da kwamitin da zai sa ido a kan asusun tallafa wa mutanen da hare-haren Boko Haram suka shafa a kasar.

Kwamitin zai tantance wadanda abin ya shafa, sannan kuma ya taimaka musu.

A mafi yawancin lokuta wadanda rikicin Boko Haram din ya shafa na zargin gwamnati da yin watsi da su a lokacin da suke fuskantar mawuyacin hali.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin ba lallai ne wadanda aka yi dominsu su gani a kasa suna ba da misali da asusun tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da aka taba kafa wa a kasar.