'Na so na gana da Shugaba Jonathan'

Rabecca Samuel da Malala Yousefzai
Image caption Rabecca Samuel da Malala Yousefzai

Daya daga cikin iyayen yaran da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace ta ce ta so ta gana da Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan a ranar Talata amma 'ya'yan kungiyar al'ummar Chibok mazauna Abuja suka hana ganawar.

Madam Rabecca Samuel ta bayyana cewa ita a matsayinta na uwa, bata da damar zuwa gaba gadi ta gana da shugaban kasar ba tare da amincewar yan kungiyar tasu ba.

Madam Rabecca Samuel ta shaidawa BBC cewa 'yan kungiyar sun dage akan cewar, bai kamata iyayen yara su 9 da suka zo Abuja domin ganawa da Malala Yousefzai su gana tare da shugaban kasa ba tare da amincewar sauran iyayen yaran da ke Chibok ba.

'Yan kungiyar ta 'yan Chibok mazauna Abuja sun gabatar da hujjar cewar iyaye 9 da kuma 'yan mata 5 da suka tsere bayan 'yan kungiyar Boko Haram ta kamasu bai kamata su wakilci sauran iyayen ba.

Wasu daga cikin shugabannin al'umomin Chibok, sun bayyan rashin jin dadinsu akan yadda sai da Malala ta gabatar da bukata a gaban Shugaban Kasa sannan ya amince da ya gana da su, suna masu cewar, menene daliin da za'a dauki kwanaki 92 gabanin Shugaban kasar ya ce zai gana da su.

Tuni fadar Shugaban Kasar Nigeriar ta soki 'yan kungiyar nan da ke fafutukar ceto 'yan matan da aka sace wato #BringBackOurGirls da amfani da siyasa akan takaicin da iyayen yaran da aka sace suke fama da shi.