An sace Bajamushe a jahar Adamawa

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun yi amfani da babura wajen sace wani Bajamushe a shiyyar arewa maso-gabashin Najeriya.

An ba da labarin cewa mutumin yana aiki ne a wata cibiyar ilimantar da matasa da ke garin Gombi a jihar Adamawa.

An ruwaito cewa da sanyin safiya 'yan bindigar suka tsare Bajamushen a motarsa, suna masa magana da harshen Hausa alhali ba ya ji.

Daga nan suka yi awon gaba da shi a kan babur.

Wani jami'in 'yan sanda a yankin ya ce jami'ansu sun bazama wajen nemo barayin don ceton Bajamushen.

Sace mutane ana garkuwa da su a Nijeriya wata babbar matsala ce musamman a kudancin kasar.

Amma ga alama a baya-bayan nan matsalar na karuwa a arewacin kasar sakamakon tabarbarewar tsaro.