Isra'ila na ci gaba kai hari a Gaza

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane kusan 200 Isra'ila ta kashe a kwanakin nan a Gaza

Isra'ila ta kara kaimi a hare-haren da take kaiwa kan zirin-Gaza, a daidai lokacin da jami'an gwamnatin kasar ke kira da ta kai wa yankin hari ta kasa.

A kalla Falasdinawa bakwai ne aka kashe a hare-haren da Isra'ilar ta kai da asubar fari a ranar Larabar nan, kuma an gargadi dubban mutane da su fice daga gidajensu da ke garin Beit Lahiya, da wasu biyu da ke makwabtaka da Gaza.

Al'ummar yankin sun ce sun shiga tsaka mai wuya.

Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Natanyahu ya kori ministan tsaron kasar a ranar Talata, saboda ya tsaya kai-da-fata sai an kai hari ta kasa.

Ana sa ran shugaban Falasdnawa, Mahmud Abbas ya isa Masar domin tattaunawa da mahukuntan kasar a kan wannan rikicin.

Karin bayani