Isra'ila za ta tsagaita bude wuta a Gaza

Gaza Hakkin mallakar hoto
Image caption Gaza

Isra'ila ta sanar da dakatar da bude wuta a Gaza saboda dalilai irin na jin kai.

Wannan mataki dai ya biyo bayan wata bukata da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar ne.

Wani jami'in Majalisar ya shaida wa BBC cewa za ta fara dakatar da bude wutar ne daga karfe goma na safiyar Alhamis zuwa uku na yamma.

A waje daya kuma an halaka wasu yara hudu Palasdinawa 'yan gida daya, a hare-haren bom din da Isra'ila ke kaiwa Gazar, yayin da yaran ke wasa a bakin Teku.

Sun mutu ne a gaban wani Otel din da 'yan jarida daga kasashen waje ke sauka.

Bangaren mayakan kungiyar Hamas ya bayyana harin da cewa aikata laifukan yaki ne.

Sojojin Isra'ila sun ce za su gudanar da bincike a kan abin da ya faru, suna dora alhakin lamarin kan kungiyar ta Hamas.