An kafa asusun tallafi kan rikicin Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan ya ce 'yan Boko Haram za su gane kuskurensu

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya kaddamar da asusu domin tallafa wa mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa.

Da yake kaddamar da asusun, Mista Jonathan ya ce ya yi hakan ne domin saukaka wa mutanen da hare-haren 'yan ta'adda suka shafa kai-tsaye.

A cewarsa, koda yake ta'addanci ba al'amari ne da ake addu'ar aukuwarsa ba, ya zama wajibi a tallafa wa mutanen da al'amarin ya shafa.

Mista Jonathan ya ce mutanen da ke kashe jama'a babu gaira babu dalili za su gane kuskurensu komai daren dadewa.

Karin bayani