Hollande ya soma ziyara a Afrika

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Francois Hollande

Shugaban Faransa Francois Hollande ya fara ziyarar kwanaki uku a wasu kasashe na yammacin Afirka.

Ziyarar za ta maida hankali ne a kan batun tsaro da kuma dangantakar tattalin arziki.

Shugaba Hollande ya fara ya da zango ne a kasar Ivory Coast tare da rakiyar manyan 'yan kasuwar Faransa kimanin hamsin.

Kasar Faransa dai har yanzu tana da muhimman muradun tattalin arziki a Afirka kuma kamfanonin kasar da dama suna gudanar da harkokin kasuwanci a Ivory Coast.

Bayan kasar ta Ivory Coast, Hollande zai kai ziyara Niger yayin da a ranar Asabar kuma ya ziyarci kasar Chadi.