Boko Haram: Jonathan zai ranto $ 1 bn

Image caption Dubban 'yan Najeriya ne suka rasa rayukansu da dukiyoyi sakamakon rikicin Boko Haram

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya nemi amincewar majalisar dokokin kasar, saboda ya aro $1 biliyan domin yaki da kungiyar Boko Haram.

A wasikun da ya tura majalisar wakilai da ta dattijai, shugaban ya ce akwai bukatar gaggawa na bai wa jami'an tsaro makamai masu inganci tare da horo da kuma sauran kayayyakin aiki ta yadda za su iya fuskantar barazanar kungiyar.

A watan Fabrairu ne dai gwamnan jihar Borno, tungar Boko Haram ya ce 'yan kungiyar sun fi jami'an tsaron Najeriya makamai da kuma samun kwarin gwiwa.

Sai dai gwamnatin tarayya da kuma rundunar tsaro sun fito sun musanta abin da Kashim Shettiman ya fada.