Microsoft zai sallami ma'aikata 18,000

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Galibin ma'aikatan da za a kora na bangaren Nokia ne

Kamfanin manhaja na Micrososft zai rage guraben ayyuka 18,000 a fadin duniya, wato kusan kashi 15 na ma'aikatansa nan da shekara mai zuwa.

Kimanin dubu 12 da rabi daga cikin ma'aikatan zai zaftare su ne a sashen wayarsa na Nokia, wanda Micrososft ya saya a watan Afrilu.

Wannan ne rage ma'aikata mafi girma a shekaru 39 na tarihin kamfanin, yayin da ya ke shirin gogayya da kamfanonin Apple da Google.

Shugabar Satya Nadella wadda ta karbi ragamar kamfanin a farkon wannan shekarar na son microsoft ya maida hankali a kan ayyukan da suka shafi intanet.

Ragin ma'aikatan dai sun rubanya wanda kamafinin ya yi a shekarar 2009 har sau uku.