An gamu da cikas a yaki da cutar Aids

Hakkin mallakar hoto AFP

Fasinjoji da dama da suka mutu a cikin jirgin nan da yai hatsari na Malaysia, ana tunanin suna kan hanyarsu ne ta zuwa babban taron Kasashen duniya akan cutar Aids

Sun hada da Farfesa Joep Lange- wani fitacce kuma sanannen mai bincike kuma tsohon Shugaban kungiyar yaki da cutar Aids ta kasashen duniya wato IAS

Kungiyar IAS tace sun yi babban rashi

Wakilai wadanda suka isa wurin babban Taron a Australia sunce sun gigita sosai

Masana kimiyya fiye da 14,000 da masu fafutuka da 'yan siyasa na ganawa a babban taron na Aids na shekarar 2014 wanda ake farawa a Melbourne a karshen mako

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Prof Joep Lange ya mutu a hatsarin jirgin

Joep Lange, shehin malamin bangaren aikin likita ne a jami'ar Amsterdam kuma ya kasance yana binciken cutar HIV tun lokacin da kwayar cutar ta bullo a shekarun 1980s

Ya samar da magungunan rage kaifin kwayar cutar wanda suka taimakawa masu fama da cutar

Ya kuma yi aiki wajen tabbatar da cewa uwa wacce take dauke da kwayar cutar bata harbawa dan cikinta kwayar cutar ba a lokacin da take dauke da juna biyu ko kuma cikin ciwon haihuwa

An bayyana Farfesa Lange a matsayin wani shugaba a bangaren da ya kware, kuma tsakanin shekarar 2002 da 2004 shine Shugaban kungiyar yaki da cutar Aids ta kasashen duniya

Farfesa Riess wanda shima yai aiki a jami'ar Amsterdam ya fadawa BBC cewa " Joep abokin aikine na kut da kut kuma kowa a nan Melbourne ya gigita da labarin abinda ya faru".

"A farkon shekarun 1980 lokacin da wannan bakuwar cuta ta bujurowa Amsterdam ni da Joep na samun horo a wannan lokacin, a saboda haka aka tunkare mu da wannan sabuwar cuta wacce ta sa muka dukufa wajen aikin bincike da samar da magani".