'Yan Boko Haram sun kafa tutoci a Damboa

Mayakan kungiyar Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram

Rahatanni daga garin Damboa na jahar Borno na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kwace garin baki daya, har ma kuma sun kafa tutocinsu a ko'ina cikinsa.

Hakan dai ya biyo bayan wani hari ne da yan kungiyar suka kai a garin ne wanda kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane da yawa tare kuma da kona wasu sassan garin.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewar wasu mutanen garin sun koma Biu yayinda wasu kuma suka tsere suka samu kaiwa Maiduguri.

Ya ce don haka a yanzu duk wadanda ke a cikin garin yan kungiyar ta Boko Haram ne, sun kafa tutocinsu , sun kuma kori kowa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da a garin N'gala da ke arewacin jahar Borno 'yan kungiyar ta Boko Haram suka yi awon gaba da matar wani mai bada shawara a karamar hukumar ta N'gala da kuma 'yar shi mai kimanin shekaru goma, bayan da suka je nemansa ba su same shi ba.

Lamarin sace sacen mata dai a Najeriya musamman a jahar ta Borno sai kara kamari ya ke tun bayan da yan kungiyar Boko Haram din suka sace 'yan matan makarantar Sakandiren garin Chibok su fiye da dari biyu, yau fiye da watanni uku kenan.

Rahotanni daga garin Damboa na jihar Borno na cewa wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne, sun kashe mutane da dama tare da kona gidaje masu yawa a garin.

Wasu da suka tsira a harin sun ce ba a kai ga tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba.

A farkon wannan watan ne 'yan Boko Haram din suka kai hari a kan wani barikin sojoji da ke wajen garin Damboa inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

A cikin wannan makon, 'yan Boko Haram sun kashe mutane kusan 45 a kauyen Dille da ke jihar ta Borno.

Kungiyar Boko Haram ta hallaka mutane fiye da 2,000 a wannan shekarar.