'Za a yi yakin neman zabe da bashin sayen makamai'

 Shugaban Najeriya Good luck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya Good luck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya aika wa Majalisar Dattawan kasar da wata wasika inda ya ke neman da ta amince masu karbo bashin Sama da dala biliyan daya kimanin Naira biliyan 165 daga kasashen waje domin yaki da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

A cikin wasikar da ya aika zuwa ga Shugaban Majalisar Sanata David Mark, Mr. Jonathan ya ce ana bukatar bashin ne domin yi wa makamai sojoji da sauran jami'an tsaro garambawul da kuma ba su horo ta yadda za su iya tunkarar barazanar ta'addanci a kasar.

To, sai dai, Alhaji Abubakar Tsav, wani mai sharhi kan lamurran tsaro a kasar ta Najeriya ya ce, bashin da ake neman karba, ana so ne kawai a yi amfani da kudin wajen yakin neman zabe.

Karin bayani