Boko Haram: An samu cikas a yunkurin karbo bashi

Image caption An Boko Haram da aka kama a Sambisa

Majalisar dokokin Nigeria ta soma hutu na watanni biyu, abin da ke nufin cewa za a dauki lokaci mai tsawo kafin ta amince da batun bashin da kasar za ta karbo don yaki da Boko Haram.

A cikin wannan makon ne Shugaba Goodluck Jonathan ya mika wa majalisun takardar bukatar neman izini, domin gwamnati ta karbo bashin dala biliyan daya domin sayo abubuwan da soji za su bukata a kokarin yaki da Boko Haram.

Hakan na nufin cewa bukatar Mr Jonathan ta gamu da cikas, domin dole ne ya jira kafin ya samu damar karbo bashin.

Gwamnatin Jonathan na fuskantar suka game da kasa magance matsalar kungiyar Boko Haram.

Kungiyar ta sace 'yan mata dalibai fiye da 200 a garin Chibok a cikin watan Afrilu kuma kawo yanzu gwamnati ta kasa kubutar da su.

Masu sukar gwamnati na zargin cewa cin hanci da rashawa ne ya hana al'ummar kasar ta ga tasirin kusan dala biliyan shida da aka kebe a kasafin kudin bana domin magance matsalar tsaro a kasar.

Sai a cikin watan Satumba ne ake sa ran Majalisar wakilai da ta Dattijai za su koma bakin aiki.