AIDS na karuwa tsakanin 'yan luwadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Da yawa daga cikin wadanda suka mutu a hadarin jirgin saman Malaysia kwararru ne da masu yaki da cutar AIDS.

Yawan sababbin masu kamuwa da kwayar cutar AIDS ko wato kanjamau a tsakanin matasa maza 'yan luwadi ya linka a Amurka a cikin shekaru goma.

Sai dai kuma yawan mutanen da ke kamuwa da cuta me karya garkuwar jikin, a Amurkan, ya ragu da kashi daya bisa uku, a tsawon lokacin, kamar a sauran kasashen duniya.

Sakamakon binciken, na alkaluman da aka tattara ne daga jihohin Amurkan 50, tsakanin shekara ta 2002 da 2011.

An kuma bayyana shi ne, domin yazo dai-dai da lokacin da ake taron kasashen duniya kan cutar ta AIDS ko a Melbourne da ke Australia, wanda za a fara ranar Lahadi.