Sojin Isra'ila biyu sun mutu a artabu da Falasdinawa

Sojin Isra'ila a Gaza Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojin Isra'ila a Gaza

Wasu sojoin Israila biyu sun rasa rayukansu yayin wata arangama da Falasdinawa wadanda suka kutsa Isra'ilar daga Gaza.

Sojin Israila sun ce 'yan gwagwarmayar Falasdinawa akalla tara ne suke kyautata tsammanin sun shiga Isra'ilar ta wata hanya karkashin kasa kuma sun doshi wani yanki na Yahudawa dauke da manyan bindigogi.

A waje guda kuma wani gangamin masu zanga zangar magoya bayan Falasdinawa sun yi arangama da 'yan sanda a Paris babban birnin Faransa inda suka yi bujire wa haramcin da hukumomin suka sanya a kan wani taron gangami na nuna goyon baya ga al'ummar Gaza.

Masu zanga zangar sun yi ta jifa da duwatsu yayin da yan sanda suka rika harba musu hayaki mai sa kwalla.

Wasu masu zanga zangar na fadin Allah ya ja zamanin Falasdinu yayin da wasu kuma ke tir da Allah wadai da Isra'ila.