Shugaba Jonathan zai je Chibok - Inji Gwamnatin Najeriya

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewar a shirye shugaban kasar Goodluck Jonathan ya ke ya je yankin Chibok a ko da yaushe duk da cewa a halin yanzu iyalan 'yan matan da aka sace na kan hanyar su zuwa Abuja domin ganawa da shugaban.

Mista Mike Omeri shugaban cibiyar samar da bayanai kan al'amuran ta'adanci shi ya fadi hakan a cikin wata hira da wakilinmu.

Mista Omeri ya ce,yanzu haka iyayen yaran yan matan na Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace na kan hanyarsu ta zuwa Abuja domin ganawa da shugaban kasar.

Ya ce Wannan ganawa ce dai ta haddasa samun rarrabuwar kawuna tsakanin iyayen 'yan matan Chibok .

A yayin da wasu ke ganin Iyayen 'yan matan da suka dawo gida ne ya kamata su gana da shugaban kasar, a nasu bangare Iyayen 'yan matan da har yanzu basu dawo gida ba sun ce su ne suka cancanta a yi ganawar da su.

Wani daga cikin iyayen da aka sace ya'yan nasu ya ce ga alama an saka siyasa a cikin lamarin tare da cewar a dauko mutane uku -uku daga kowace mazaba domin tafiyar Abuja.

A cikin mako mai zuwa ne dai yan matan za su cika kwanaki dari cif a hannun wadanda suka sace su.