Kiristoci a Mosul sun koka da korar su

Mujami'ar Kiristoci a Iraqi Hakkin mallakar hoto
Image caption Mujami'ar Kiristoci a Iraqi

Wani babban bishop a Iraqi ya yi kira ga kasashen duniya su dauki mataki bayan da masu fafutukar musulunci suka fatattaki daruruwan Kiristoci daga gidajensu a garin Mosul,

lamarin da yace ya kawo karshen zaman Kiristoci wadanda suka shafe kusan shekaru dubu biyu suna zaure a wurin.

A watan da ya gabata ne yan kungiyar ISIS masu fafutukar musulunci wadanda suka kwace birnin Mosul suka bada wa'adi ga dukkann Kiristoci inda suka tilasta musu su karbi musulunci ko su biya jiziya ko kuma su bar kasar.

Bishop din Shlemon Warduni wanda ke wakiltar wani tsohon reshe na gargajiya na mabiya addinin Kiristar ya ce Kiristoci sun rasa dukkanin abin da suka mallaka.

Yana mai baiyana takaici cewa shugabannin sauran addinai a Iraqi ba su ce komai domin kare su ba.

A birnin Rome Fafaroma Francis ya yi adduoi ga iyalan Kiristocin da aka kora

Karin bayani