Gaza: Majalisar Dinkin Duniya 'ta damu'

Hakkin mallakar hoto AFP GETTY
Image caption An kashe fiye da mutane 100 a unguwar daya kawai ta Shija'iyyah.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa ga yadda adadin wadanda ke mutuwa da samun raunukka ke dada hauhawa a Gaza inda yayi kiran tsagaita wuta nan take.

Bayan wani taron gaggawa da kwamitin yayi cikin dare, jakadan Rwanda a Majalisar ta Dinkin Duniya wanda ke shugabantar kwamitin ya ce wakilan kwamitin sun yi kiran da a mutunta dokokin kasa-da-kasa da suka shafi kare fararen hulla.

Tun farko Sakataren Majalisar ta dinkin duniya Ban Ki Moon ya bayyana hare-haren da Isra'ila ta kai kan unguwa mai cunkoson jama'a ta Shuja'iyyah da cewa na zalunci da rashin imani ne.

Falasdinawa fiye 500 ne suka mutu ya zuwa yanzu a cikin hare-haren sojojin Isra'ila suka kaddamar kan Zirin Gaza makonni biyun da suka wuce, yayinda aka kashe sojojin Isra'ilan 18 da fareren hulla 2.

Karin bayani