An kama 'yar shekara goma da jigidar bam a Funtua

Abubakar Shekau, Shugaban Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau, Shugaban Boko Haram

Gwamnatin Najeriyar ta ce ta kama wata yarinya yar shekara goma da bama bama daure a jikinta a Funtua ta Jihar Katsina.

A wajen wani bayani yau a Abuja shugaban cibiyar bayar da bayanai kan ayyukan ta'addanci a Najeriyar Mr Mike Omeri,ya ce jami'an tsaro sun tsayar da wata karamar mota, inda suka kama wasu su 3 da ake zargin yan Boko Haram ne.

Mr Omeri ya ce gungun mutanen ya hada da namiji daya da yan mata biyu, masu shekaru 18 da goma. Mr Omeri ya ce biyun masu shekarun da suka dara sun yi kokarin su tsere.

Ya ce a nan ne aka gano yarinyar mai shekaru goma daure da jigidar bama bamai.

A halin da ake ciki kuma Kakakin yansandan Najeriya Franl Mba ya ce, manyan kungiyoyin yan ta'adda na yin amfani da mata a matsayin yan kunar bakin wake saboda ba kasafai akan zargi mata ba.

Mummunan hanyar tura yan mata a matsayin yan kunar bakin wake dai ta fara ne watanni ukku da rabi bayan da Boko Haram ta sace yan makaranta yan mata fiye da dari biyu a garin Chibok na Jihar Borno.