Kenya: 'Yan bindiga sun hallaka jama'a

Image caption Kungiyar al Shabaab ake dora wa alhakin yawancin hare haren na Kenya

Wasu 'yan bindiga akan babura sun kai hari inda suka kashe mutane akalla hudu suka lahanta wasu da dama a birnin Mombasa na Kenya.

An ruwaito 'yan sanda na cewa 'yan bindigar sun bude wuta kan jama'ar da ke wucewa, suka rika harbin kan mai-uwa-da-wabi.

Birnin mai tashar jirgin ruwa ya yi fama da tashe tashen hankali, na harin bama bamai da bindiga a cikin watannin nan.

Hare haren da yawanci ake dangantawa da kungiyar al Shabaab ta Somalia, wadda ke cewa tana kai su ne domin mayar da martani na shigar sojin Kenya rikicin Somalia.