Boko Haram: Mutane 20 sun mutu a Digire

Sojin Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojin Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane akalla ashirin ne suka mutu a garin Digire da ke jahar Borno kusa da iyakar kasar da ta Kamaru cikin wani dauki ba dadi tsakanin hadakar jami'an tsaron Najeriya da na Kamarun bangare guda da kuma 'yan kungiyar Boko Haram a gudan bangaren.

Jami'an tsaron sun yi nasarar kama wasu da ake kyautata cewa 'yan kungiyar ne ta Boko Haram tare da kwace motocin su.

A garin Kalabalge ma rahotanni na cewa 'yan kungiyar busa babura sun kai hari tare da kona wasu wurare na gwamnati da dama a daren jiya .

Wani mazaunin garin ya ce maharan sun fatattake su , suka sheka daji inda suka kwana a can cikin ruwan sama.